logo

HAUSA

Sin na goyon bayan Kwamitin Sulhu ya dauki kwakkwaran mataki kan batun Gabas ta Tsakiya

2024-11-19 14:21:34 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Fu Cong, ya ce yankin Gabas ta Tsakiya na cikin wani mawuyacin hali, yana mai kira ga dukkan mambobin Kwamitin Sulhu na MDD da su hada kai su marawa Kwamitin baya wajen daukar kwakkwaran mataki kan batun.

Fu Cong ya bayyana haka ne jiya Litinin, yayin taron manyan jami’ai na Kwamitin Sulhu na MDD don gane da batun Gabas ta Tsakiya.

Wakilin na Sin ya ce cikin watanni 13 da suka gabata, rikicin Gaza da yanayin da Gabas ta Tsakiya ke ciki shi ke daukar matsayi mai muhimmanci cikin ajandar kwamitin. Ya ce an tattauna akai-akai, amma yanayin ya kara tsananta. Yana mai cewa ba don Amurka ta yi ta hawa kujerar na ki ko ikirarin cewa kudurorin kwamitin ba su da karfin doka ba, da Kwamitin Sulhun bai rasa karfinsa. Haka kuma, da Amurka ba ta ci gaba da samar da makamai ba, da yakin bai tsawaita haka ba.

Fu Cong ya kara da cewa, kasashen 10 wadanda ba mambobin kwamitin na dindindin ba, sun gabatar da daftarin kudurin dake kira da a dakatar da bude wuta ba tare da bata lokaci ba a Zirin Gaza, wanda ya wakilci sabon zagaye na kokarin Kwamitin na dakatar da yaki da kuma dawo da zaman lafiya. Bugu da kari, ya ce kasar Sin tana goyon bayan Kwamitin Sulhun ya gaggauta zartar da wannan kuduri. (Fa’iza Mustapha)