Kasashen duniya suna sa ran jin muryoyin kasar Sin a taron kolin G20
2024-11-19 01:40:25 CMG Hausa
Ana gudanar da taron kolin shugabannin kungiyar G20 karo na 19 daga ranar 18 zuwa ranar 19 ga watan da muke ciki, a birnin Rio de Janeiro dake kasar Brazil. Jigon taron shi ne “gina duniya mai adalci da ci gaba mai dorewa”.
A cikin kwanakin nan, kasashen duniya sun bayyana fatansu na ganin Sin ta ba da sabbin damammaki na samar da ci gaba ga duniya a taron kolin G20 na wannan karo.
Samun ci gaba, abu ne mai muhimmanci ga ko wace kasa. A karkashin hadin gwiwar kasashen G20, Sin ta dade tana mai da hankali kan batun ci gaba, ta fitar da kuma aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya tare da shawarar bunkasa duniya da aka san ta da GDI, sannan tana maraba da kasashen mambobin G20 su shiga hadin gwiwa bisa shawarwarin, ta yadda za a tabbatar da ci gaban duniya tare.
A cikin rukunin aiki na “yaki da yunwa da talauci” da kasar dake shugabancin taron kolin G20 na wannan karo wato kasar Brazil ta kafa, sau da dama ne Sin ta raba dabarunta na rage talauci da kirkire-kirkiren fasahohi, har ta kasance daya daga cikin kasashe mafi ba da gudunmawa. Ban da haka, abin da aka lura shi ne Sin ta dade tana jadadda samun ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire, musamman ma a fannin tattalin arziki na zamani da samun ci gaba mara gurbata muhalli. A sa’i daya kuma, wata ajanda mai muhimmanci ta taron kolin G20 na wannan karo ita ce tattauna samun ci gaba ta fuskar rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi. Wannan ya sa kasashen duniya ke fatan ganin Sin za ta samar da babban kuzari wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa a duniya.
A karkashin tsarin kungiyar G20, Sin ta sha yin kira da a aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban, da kuma tsayawa tsayin-daka kan ra’ayin tattaunawa tare, da ginawa tare, da kuma rabawa tare wajen gudanar da harkokin duniya. Kasar Sin tana kuma sa kaimin tabbatar da karin gaskiya da adalci a wajen tafiyar da harkokin tattalin arzikin duniya, tare da kara fitowa da muryoyin kasashe masu tasowa.
Yayin taron kolin, Sin za ta tattauna batun samun ci gaba tare da bangarorin kasashe daban-daban, da kuma kira da karfafa kasancewar bangarori daban ddaban a duniya da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya. Saboda hakan, kasashen duniya suna fatan Sin za ta taimaka da basira da karfinta na samun ci gaba tare da inganta mulkin kasa da kasa ga kasashen duniya.(Safiyah Ma)