logo

HAUSA

Sin ta gaggauta bunkasuwar duniya baki daya ta amfani da damammaki masu kyau a taron G20

2024-11-19 23:57:35 CMG Hausa

A gun taron koli na G20 na wannan karo, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da manyan matakai 8 na goyon bayan raya duniya, ciki har da raya shawarar “ziri daya da hanya daya” mai inganci cikin hadin kai da zurfafa hakikanin hadin kai a fannonin da suka shafi kawar da talauci da samar da isashen hatsi da tattalin arziki na zamani da dai sauransu, kana da goyon bayan bunkasuwar nahiyar Afirka da habaka bude kofa ga kasashe mafi karancin bunkasuwa da sauransu, dukkan matakan na la’akari da ainihin abubuwan da ake bukata.

Ban da wannan kuma, Sin ta yanke shawarar shiga kawancen yaki da yunwa da talauci a duniya da Brazil mai rike da shugabancin taron na wannan karo ta gabatar.

Wadannan abubuwa sun bayyana cewa, kasancewar Sin kasa mai daukar ainihin mataki wajen goyon bayan raya kasashe masu tasowa, abin da take yi shi ne nacewa ga hadin gwiwa da sauran kasashe don kawar da talauci da tabbatar da kyakkyawar fatan Bil Adam baki daya. (Amina Xu)