logo

HAUSA

Gwamnatin Sudan: Kofa a bude take domin warware rikici da kai kayayyakin agaji

2024-11-19 10:11:11 CMG Hausa

Gwamnatin Sudan ta ce kofarta a bude take ga dukkan mafitar da za ta warware rikicin kasar, da bayar da damar shigar da kayayyakin agaji, sai dai kuma ba ta amince a yi amfani da wannan dama wajen kai makamai ga ‘yan tawaye, maimakon samar da kayayyakin abinci ba.

Jakadan Sudan a Amurka Mohamed Abdullah, ya ruwaito shugaban gwamnatin riko kuma kwamandan rundunar sojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan ne ya bayyana haka jiya Litinin, yayin ganawarsa da manzon musammaman na Amurka a Sudan Tom Perriello, dake ziyara a kasar.

Jakada Abdullah, ya ce Al-Burhan ya shaidawa Perriello cewa, gwamnatin Sudan ba ta amince a yi amfani da iyakar Adre dake tsakaninta da kasar Chadi wajen kai makamai ga dakarun sa kai na RSF ba. (Fa’iza Mustapha)