Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce sauye-sauyen tattalin arziki da ake yi zai kawo karshen talauci a kasar
2024-11-19 08:14:38 CMG Hausa
Gwamnatin tarayyar Najeriya tana da kwarin gwiwar cewa sauye-sauyen da ake kan yi yanzu haka a manufofin tattalin arzikin kasar zai taimakawa wajen kawo karshen matsalar talauci a tsakanin al’umma, sannan kuma zai samar da kyakkyawan ginshiki ga ci gaban masana’antu da harkokin zuba jari.
Ministan kudi na kasar Mr. Wale Edun ne ya tabbatar da hakan jiya Litinin 18 ga wata a jawabin da ya gabatar wajen bude babban taron kasa a kan harkokin kudi da ci gaban tattalin arziki na 2024 a garin Bauchi .
Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Mr. Wale Edun wanda ya bayyana babban taro a matsayin wani dandali da zai bayar da damar fahimtar halin da ake ciki ta fuskar tattalin arziki, da irin albarkatun da kasa ke da su kana kuma da sanin irin kwararrun da ake da su a kasa.
Haka kuma ministan ya ce, taron zai haskawa gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki bangarorin da za a iya yin aikin hadin gwiwa da kuma wanda kuma daidaiku za su iya yi domin dai kasar ta samu sukunin amfana da dinbin arzikinta, ya kuma yabawa gwamnatin jihar Bauchi bisa daukar nauyin gudanar da shi wannan taron.
A jawabinsa, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad jaddada mahimmancin hada kai ya yi domin shawo kan kalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta, a don haka ya yi fatan mahalarta taron za su fito da shawarwari ingantattu da za su taimakawa gwamnatin tarayya a sauye-sauyen da take yi a tsarin tattalin arzikin kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)