Babu Wata Kasa Da Za Ta Ce ''Ita Kadai Ta Isa Gayya''
2024-11-19 16:02:35 CMG Hausa
An yi zama na II na taron kungiyar G20 karo na 19 a jiya Litinin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken ''Hada Hannu Domin Tafiyar da Tsarin Tattalin Arzikin Duniya Bisa Adalci da Daidaito''.
A ra'ayina, wannan jawabi ya gabatar da shawarwari da hanya mai sauki ta shawo kan matsalolin tattalin arziki da duniya ke fama da su, har ma da hanyoyin da kasashe za su iya hada hannu domin taimakon juna.
Daga cikin kalaman shugaba Xi, akwai wadanda suka fi jan hankalina, inda yake cewa, ya kamata a yi adawa da kariyar cinikayya da ra'ayin bangare daya da sanya yarjejeniyar saukaka zuba jari domin samun ci gaba, cikin tsarin dokokin WTO.
Zan iya cewa, cikin wadannan kalamai kalilan, shugaban ya gabatar da mafita mafi sauki ga matsalolin duniya. Idan muka dauki batun kariyar cinikayya da zartar da ra'ayin bangare guda da wasu kasashen duniya ke ganin su ne mafita gare su, mun riga mun ga yadda hakan bai amfanawa kowannne bangare da komai ba. Ci gaban wata kasa, dama ce ga sauran kasashen duniya maimakon barazana ko kalubale. Mun riga mun gane cewa, babu wata kasa da za ta iya cewa za ta raba gari da wata, domin makomar kasashen na hade da juna. Idan wata na fama da talauci ko matsaloli, to wadannan matsaloli na iya bazuwa ga sauran, haka ma idan tana cikin wadata da kwanciyar hankali. Idan muka dauki Sin a matsayin misali, muhimmiyar rawar da take takawa wajen samarwa duniya damarmaki da dimbin gudunmuwarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya, abu ne da ba zai misaltu ba, don haka, babu wata kasa da za ta ce ta yanke mu'amala da ita ko kuma ta bugi kirjin cewa ita kadai (kasar) ta isa gayya.
Idan har ba neman fifiko ko mulkin danniya ba, to mene ne dalilin wariya ko kariyar cinikayya tsakanin kasashe bayan mafita ita ce hada hannu tsakaninsu domin cin moriyar juna? A wannan zamani da ake ciki, ba zai yuwu duniya ta ci gaba da kasancewa karkashin ikon wata kasa daya ko wasu kasashe kalilan ba, dole ne irin wadannan kasashe su zubar da girman kai su hada kai da sauran takwarorinsu domin ceto duniya daga fadawa mummunan yanayi. (Fa'iza Musatapha)