APEC: Nisan Wuri Ba Ya Hana Sada Zumunci Da Kulla Alheri Tsakanin Sin Da Kasashen Duniya
2024-11-18 14:30:04 CMG Hausa
Tun ana sauran mako guda a gudanar da taron shugabannin tattalin arzikin Kungiyar Hadin Gwiwar Asiya da Yankin Tekun Fasifik wato APEC, karo na 31, wanda aka kamala ranar 16 ga Nuwamban nan, kafofin watsa labarai na duniya suka yi ta yayata batun taron musamman a kasashen da abin ya shafa.
Hadin gwiwar da ya haifar da kafuwar kungiyar APEC a shekarar 1989 ya zama tamkar wani sabon-wata-sha-kallo saboda alfanun da yake tattare da shi da kuma zama wani madubi dai zai haska wa daukacin mutane masu rajin kawo sauyi da ci gaban al’ummar duniya na bai-daya irin turbar da ya dace kasashe musamman a matakin yankuna su bi domin fita daga kangin danniya da rashin makama wurin warware dabaibayin da ya hana ruwa gudu ga ci gaban tattalin arzikinsu.
Kamar yadda alkaluma suka nuna daga majiyoyi daban-daban, daga shekarar 2014 zuwa 2022, hada-hadar tattalin arzikin kasashen kungiyar ta APEC ta habaka zuwa kimanin dala tiriliyan 64.45. Wannan yana nuna kasashen ne suke da kashi 60 a cikin dari na jimillar hada-hadar tattalin arzikin duniya baki daya. Kasar Sin da ta zama kasa mai matukar muhimmanci a wannan hadin gwiwa, ta taimaka gaya da salo da kuma irin ci gaban da ta samu ga kasashen kungiyar.
Wannan ya sa lokacin da kasar ta Sin ta yi tayin karbar bakuncin taron shugabannin APEC a shekarar 2026 wanda zai zama karo na uku ke nan da za ta karbi bakuncin taron, ba a yi wata-wata ba aka amince mata. Kasashen kungiyar suna da yakinin kasar Sin ta san hanya kuma ba ta masu mugunta a kai. Tsare-tsarenta na bude kofa ba ga kawai membobin APEC ba har ma da sauran sassan duniya, sun isa su zama shaida baro-baro a fili.
Wani abin birgewa da ya haifar da karsashin motsawar tattalin arzikin kasashen hadin gwaiwar APEC shi ne yadda ake ci gaba da samun raguwar haraji madaidaici a tsakanin kasashen APEC. Abin ya ragu daga kashi 17 a cikin dari a shekarar 1989 zuwa kashi 5.3 a cikin dari a shekarar 2021. Duk wannan ya samu ne saboda saboda ci gaban da ake samu na gudanar da kasuwanci mai ’yanci a tsakaninsu.
Da yake an riga an sahale wa kasar Sin karbar bakuncin taron shugabannin tattalin arzikin APEC a shekaru biyu masu zuwa, shin me kasar take da muradin gani ne a taron. Sashen yada labarai na ma’aikatar kula da harkokin kasashen waje na kasar Sin ya yi karin haske a kai, inda ya jaddada cewa, kasar ta shirya tsaf wajen habaka sadarwa da hadin gwiwa da sauran kasashen kungiyar game da karbar bakuncin taron na APEC a 2026 domin a hadu tare a aiwatar da Kudurin Putrajaya nan da shekarar 2040.
Bugu da kari, kasar tana son ganin an zurfafa gina ci gaban al’ummomin Asiya da yankin tekun Fasifik da karfafa samar da yankin ciniki mai cikakken ’yanci da samun kyakkyawan sakamako ta hanyar yin hadin gwiwa a aikace ba da fatar baki ba, kana da sanya sabon kuzari ga bunkasa tattalin arzikin Asiya da yankin Fasifik.
Idan muka waiwaya ga batun sada zumunci da dunkulewar duniya wuri daya bisa kyakkawar fahimta da cin moriyar juna kuma, za mu fahimci wannan hadin gwiwa na APEC yana kara nuna wa kowa da kowa cewa bai kamata nisan wuri ya zama silar kange samun hulda mai alfanu a tsakanin kasashe ba.
Mai karatu, ko ka san cewa tsakanin Sin da birnin Lima na kasar Peru da aka gudanar da taron shugabannin APEC karo na 31 ya kai tsawon kilomita 17,000? Amma hakan bai hana kulluwar kyakkyawar alakar Sin da yankin tekun Fasifik ba. Hakan ya kuma kara fito da aniyar kasar Sin a fili game da cewa ko a wace kurya kasa ko yanki yake a duniya matukar suna son ci gaba, kofar kasar a bude take wajen rungumar juna don a-tafi-tare-a-kuma-tsira-tare!( Abdulrazaq Yahuza Jere)