An fara kada kuri’u a zaben ’yan majalissar dokokin kasar Senegal
2024-11-18 09:49:17 CMG Hausa
Da misalin karfe 8 na safiyar jiya Lahadi bisa agogon kasar Senegal ne aka bude rumfunan zaben ’yan majalissar dokokin kasar.
Ana sa ran masu kada kuri’a 7,371,890 za su yi zabe a rumfuna 7,048, da cibiyoyin kada kuri’u 16,440 dake cikin kasar da ma kasashen ketare.
Gungun kungiyoyi, da jam’iyyu ko gamayyar jam’iyyun siyasar kasar 41 ne za su fafata a zaben na wannan karo, inda za a zabi ’yan majalissun dokoki 165, don yin wakilci na wa’adin shekaru 5. (Saminu Alhassan)