logo

HAUSA

Jiang Zhenfeng dake kokarin samar da shinkafa mai inganci

2024-11-18 22:16:00 CMG Hausa

Jiang Zhenfeng, shugabar kamfanin samar da hatsi da mai na Yaozhen na lardin Hunan na kasar Sin, kuma wakiliyar babban taron wakilan mata karo na 13 na kasar Sin, da ma’aikaciyar da ta zama abun koyi a fannonin aikin gona da na karkara ta kasar. Ta jagoranci tawagar ta shuka shinkafa na tsawon shekaru goma sha biyar, kuma a yanzu haka yankin shuka shinkafa mai inganci da suke yin nazari da samarwa ya kai kusan eka dubu 7. A ko da yaushe ta kan tuna cewa samar da isassun abinci shi ne “abu mafi muhimmanci a kasa”, kuma ta himmatu wajen ganin an cika kwanon jama’ar kasar da shinkafa mai inganci da kamfaninsu ke nomawa.

To, masu sauraro a cikin shirinmu na yau za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah mai suna Jiang Zhenfeng.

An haifi Jiang Zhenfeng a cikin dangi mazauna karkara a gundumar Jianghua mai cin gashin kanta ta kabilar Yao a birnin Yongzhou na lardin Hunan dake tsakiyar kasar Sin. Mahaifinta ma’aikaci ne mai kula da tashar hatsi kuma mai duba ingancin hatsi, wanda ke son shinkafa sosai. Ta tuna cewa a lokacin girbin shinkafa, mahaifinta yana iya tantance danshi da ingancin shinkafar da hannunsa kawai. Lokacin da take karama, duk hutun lokacin zafi da na bazara, ta kan bi mahaifinta tashar hatsi kuma ta ki barinsa.

Bayan kammala karatunta daga makarantar koyar da sana’a a shekarar 1997, an tura Jiang Zhenfeng yin aiki a wani kamfani a gundumar Jianghua. A shekarar 2003, an rufe kamfanin, hakan ta rasa aikin yi. Domin ci gaba da rayuwarta, Jiang Zhenfeng ta bar garinsu ta tafi lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin don yin aiki.

A lokacin aikinta, an dora ta a bisa manufar “abinci mai tsabta”, wadda ta sa ta fito da ra’ayin komawa garinsu don fara kasuwanci, domin cimma buri din nata, ta kuma koyi dabarun noman amfanin gona. Jiang Zhenfeng ta ce, “Bisa ga karuwar matsayin zaman rayuwar al’umma, bukatun da mutane suke yi kan kayayyakin kiwon lafiya masu inganci su ma na kara karuwa, don haka, ina cike da imani na ganin an samu sakamako mai kyau kan sayar da shinkafa masu inganci a nan gaba.”

Jiang Zhenfeng ta kara da cewa, a matsayin daya daga cikin manyan larduna 13 da ake noman hatsi a kasar Sin, Hunan shi ne mafi girman yankin da ake noman shinkafa da kuma yawan amfanin gona a kasar. Ana iya cewa, lardin na da fifiko a bangaren noman shinkafa, musamman shinkafar garinsu tana girma ne a cikin tsaunuka masu zurfi, don haka suna kasancewar abinci masu tsabta, hakan ya sa suna da inganci sosai. Sai dai babu wanda ya iya fitar da irin shinkafar mai kyau daga tsaunukan.

Bayan ta koma garinsu, Jiang Zhenfeng ta tara sama da yuan dubu 10, kwatankwacin fiye da naira miliyan 2.3 na jarin kasuwanci don kafa wata masana’antar gyaran hatsi. Amma sakamakon rashin daidaito na ingancin shinkafar da suka saya, ba su iya sayar da shinkafa yadda ya kamata ba, don haka ta yanke shawarar shuka shinkafa da kanta.

A shekara ta 2009, ta ba da jinginar kadarorinta, ta aro kudi don saka hannun jari kan shuka shinkafa, ta kuma mayar da kadada 70 na gonaki zuwa shuka shinkafa. Ba kamar yadda aka saba yi ba, ta dauki hanyar shuke-shuke ta kare halittu, ta dage kan rashin amfani da magungunan kashe kwari, da kau da ciyayi da hannu.

Ko da yake yanayin da ke cikin tsaunuka yana da kyau, amma kudin da ake bukata kan kayayyakin more rayuwa, da sufuri, da sauran fannoni na da yawa, domin a yi tsimin kudi, Jiang Zhenfeng ita da kanta tana kula da komai da komai.

Hanyar neman cimma nasara ko da yaushe tana cike da cikas.

A cikin shekara ta farko, ruwan sama mai yawa da ba kasafai ake fama da shi ba, da kuma bayyanar katantanwa a cikin gonaki, sun haifar da raguwar noman shinkafa da hasara mai dimbin yawa.

A cikin shekara ta biyu, Jiang Zhenfeng ta koyi darasi daga goggagu da ta yi a baya, kuma ta samu girbin shinkafa mai yawa. Amma, saboda kudin da aka kashe wajen shuka shinkafa, da farashin shinkafa duk sun yi yawa, da kuma babban matsayin shinkafa da aka tabbatar, babu mutane da yawa ke son sayensu ba, hakan ya sanya aka gamu da matsalar sayar da shikafa.

Saboda matsin lamba da take fuskanta ta fuskar tattalin arziki sakamakon zuba jarin da ta yi na tsawon shekaru, tare da matsalolin da aka samu a tsakaninta da iyalinta sakamakon shagaltuwa da kasuwancinta, Jiang Zhenfeng ta kasance cikin matsi mai tsanani, har ma ta kasa yin barci na tsawon dare.

Amma wadanda ba su yi watsi da fatan da suke son cimmawa ba, za su iya samun sakamako mai kyau.

A watan Oktoba na shekarar 2014, da sanin cewa akwai damar halartar bikin baje kolin aikin gona na tsakiyar kasar Sin a birnin Changsha na lardin Hunan, Jiang Zhenfeng ta garzaya zuwa wurin da tawagarta ba tare da wata shakka ba.

A wajen baje kolin, ita da ’yan tawagarta sun turara shinkafa da suka shuka, tare da ba wa mahalartan da ke wucewa ta rumfar su don dandana. Shinkafar mai dadi da kamshi ta samu karbuwa a wajen kowa da kowa, sannan kuma ya taimakawa Jiang Zhenfeng wajen samun kasuwa da tallace-tallace na sayar da shinkafa.

Shinkafa mai inganci da ta shuka tun daga lokacin, ta shiga matsakaici da kananan kantuna da shaguna, da wuraren haihuwa, da gidajen cin abinci masu tsada, har ma ta fita daga lardin Hunan zuwa duk fadin kasar ta Sin.