An gudanar da tattaunawar siyasa ta bangarorin Sin da Amurka a birnin Shenzhen
2024-11-18 09:34:39 CMG Hausa
An gudanar da dandalin tattauna harkokin siyasa na bangarorin Sin da Amurka na bana a birnin Shenzhen, inda mahalarta daga bangarorin biyu suka zurfafa gudanar da managartan shawarwari, karkashin jigon "Hadin gwiwa da kalubale karkashin sabon yanayi: Tafarkin ci gaban alakar Sin da Amurka".
Yayin zaman dandalin na jiya Lahadi, sassan biyu sun amince da cewa, samar da daidaito, da yanayi mai nagarta kuma mai dorewa na alakar Sin da Amurka, zai haifar da moriyar bai daya ga kasashe 2, kana hakan ne buri guda da daukacin sassan kasa da kasa ke fatan za a cimma. (Saminu Alhassan)