logo

HAUSA

Shugaban Najeriya da na kasar Indiya sun amince da hada karfi domin tabbatar da tsaro a gabar kogin Guinea

2024-11-18 09:31:23 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinudu da takwaransa na kasar Indiya Narendra Modi sun amince su yi aiki tare domin yaki da ayyukan ta’addanci da musayar bayanan sirri.

Shugabannin biyu sun tabbatar da hakan ne jiya Lahadi 17 ga wata bayan ganawar da suka yi a birnin Abuja, a wani bangare na ziyarar da firaministan kasar ta Indiya ya kawo Najeriya bisa gayyatar shugaba Tinubu.

Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar, shugabannin sun kara jaddada aniyarsu ta hada hannu wuri guda domin karfafa alaka a bangarorin kiwon lafiya da tsaro da samar da abinci da sha’anin kimiya da fasaha da ilimi da kuma musayar al’adu.

Dukkanninsu dai sun bayyana damuwarsu a game da yadda yankin gabar kogin Guniea da kuma tekun Indiya ke fuskantar barazanar tsaro, inda suka amince da hada hannu domin samar da kariya ga hanyoyin sufuri kaya ta teku ta hanyar yakar ayyukan ’yan fashin teku.

Kasashen biyu sun kuma yi alkawarin cewa za su ci gaba da gudanar da atisayen sojin ruwa da aikin tsaron hadin gwiwa a gabar kogin Guinea musamman hanyoyin da jiragen dakon kaya ki bi.

A yayin ganawar tasu, shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yaba matuka bisa irin gudumawar da kamfanonin Indiya sama da dari 2 dake Najeriya ke bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin kasar tare kuma da samar da kofofin ayuykan yi ga ’yan kasar da damarmakin saka jari.

Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru 17 da wani shugaban kasar Indiya ya kawo ziyara Najeriya, kuma a yayin ziyarar an karrama shugaban kasar ta Indiyar Narendra Modi da lambar yabo ta GCON. (Garba Abdullahi Bagwai)