An kaddamar da katafariyar tashar tekun da aka gina bisa BRI a Peru
2024-11-17 02:24:59 CMG HAUSA
A ranar 14 ga Nuwamban da muke ciki, agogon kasar Peru ne aka kaddamar da katafariyar tashar teku ta Chancay da aka gina a kasar ta Peru.
Tashar tekun Chancay ba kawai tana da muhimmanci ba ne a karkashin hadin gwiwar Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, har ila yau ita ce irinta ta farko da aka gina aka sanya mata na’urorin aiki na zamani da kuma kiyaye lafiyar muhalli a yankin kudancin Amurka.
Bayan kammala kashin farko na aikin gina ta, za a samu raguwar dadewar fiton kaya daga Peru zuwa kasar Sin, yayin da zai koma kwanaki 23 kacal, inda hakan zai rage kudin jigilar kaya da ake kashewa da akalla kashi 20 cikin dari. (Abdulrazaq Yahuza Jere)