logo

HAUSA

Kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin APEC a shekarar 2026

2024-11-17 00:50:44 CMG HAUSA

 

Kasar Sin ce za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron da shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta yankin Asiya da teku Fasifik APEC za su gudanar a shekarar 2026.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da hakan a ranar Asabar din nan, inda ya bayyana cewa, kasarsa tana maraba da kuma tsumayar aiki tare da dukkan bangarorin da abin ya shafa wajen zurfafa hadin gwiwar yankin Asiya da tekun Fasifik domin amfanar da al’ummomin manyan yankunan guda biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)