An gudanar da bikin musayar al'adun Sin da Peru a birnin Lima
2024-11-17 08:43:32 CGTN Hausa
A ranar Juma'a 15 ga watan nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya isa birnin Lima na kasar Peru, domin halartar kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta yankin Asiya da tekun Fasifik ko APEC karo na 31, kuma yayin da yake kasar, kafar CMG ta kasar Sin, da hadin gwiwar ofishin zurfafa tattaunawa, da ofishin sakataren watsa labarai na fadar gwamnatin Peru, da kamfanin gidajen radiyo da talabijin na kasar Peru, sun shirya bikin musayar al'adun Sin da Peru a birnin Lima, fadar mulkin kasar.
Cikin wani sakon bidiyo da aka watsa, shugabar Peru Dina Boluarte, ta taya murnar nasarar bikin. Shi ma a nasa bangare, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce a ko da yaushe kamfanin CMG a shirye yake, ya ci gaba da amfanin da zarafin harsuna 81, da kusan cibiyoyin kasashen waje 200 da yake aiki da su, wajen yayata musayar al'adun Sin da na al'ummar Peru, tare da inganta amon muryoyin Peru, da na sauran kasashe masu tasowa, da masu saurin ci gaba a dandalolin tattauna batutuwan kasa da kasa. (Saminu Alhassan)