An kaddamar da tsarin taswirar Sinanci da CMG ya baiwa dakin adana kayan tarihin Larco na Peru
2024-11-17 00:06:34 CGTN
A ranar 15 ga wannan wata agogon kasar Peru, an kaddamar da tsarin taswira na harshen Sinanci da babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice ya baiwa dakin adana kayayyakin tarihi na Larco na kasar Peru kyauta a hukumance, inda shugaban CMG Shen Haixiong da shugaban dakin adana kayayyakin tarihin na Larco Andres Alvarez Calderon, da shugabar zartaswa ta dakin Ulla Holmquist Pachas suka halarci bikin tare.
A cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, dakin adana kayayyakin tarihin Larco yana mallakar kayayyakin tarihi da dama wadanda ke nuna al’adu da wayewar kan gargajiya na kasar Peru, shi ma yana wakiltar daddaden tarihin kasar ta musamman, haka kuma yana taka rawar gani wajen cudanyar al’adu tsakanin kasar Sin da Peru. Yanzu da aka kaddamar da tsarin taswira a dakin, lamarin zai kara zurfafa musayar wayewar kai tsakanin kasashen biyu, kuma masu yawon shakatawa na kasar Sin za su kara fahimtar al’adun gargajiya na kasar Peru.
A nasa bangare, shugaban dakin adana kayayyakin tarihi na Larco Andres ya yi tsokacin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a wannan karo zai kara karfin tasirin dakin adana kayayyakin tarihin a duniya, kuma zai samar da saukin fahimta ga masu bude ido da suka zo daga kasar Sin. (Jamila)