CMG ta zanta da shugaban kasar Brazil
2024-11-16 15:23:57 CMG Hausa
Albarkacin ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gudanar a kasar Brazil, da halartar taron koli karo na 19 na shugabannin kungiyar G20. Kwanan baya, wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibiji na kasar Sin wato CMG ya zanta da shugaban kasar Brazil Luiz Inácio Lula da Silva a fadar mulkinsa. Yayin zantawar, Lula ya ce, kasar ta jinjinawa huldar abota dake tsakanin kasarsa da Sin, kuma halatar Xi Jinping taron koli da za a gudanar a Brazil na da muhimmanci matuka.
Yayin da suka tabo batun yadda ajandar taron za ta dace da bukatun kasashe masu tasowa, Lula ya ce, taron zai kafa gangamin tinkarar yunwa da talauci a duniya, yana kuma mai fatan sake tattaunawa kan tsarin kudi na “Bretton Woods”, wato rawar da kungiyoyin kudade na kasa da kasa za su taka, ciki har da IMF da bankin duniya. Ya ce, wannan tsari ba ya cimma nasarar taka rawa wajen taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun kudade, maimakon haka ya zama matakin dake yin matsin lamba kan kasashe masu karancin kudaden shiga. Ya zuwa yanzu, bashin da wasu kasashen Afirka suka ci ya kai dala biliyan 900, kana kudin ruwan da suka biya ya zarce kudin da ake kashewa a fannin raya kasashen. Ya kara da cewa, yana shawartar a mai da wani kaso na basussukan da kasashen Afirka suka ci daga wajen IMF ya zama kudaden gina manyan ababen more rayuwa a kasashensu. (Amina Xu)