Wang Yi ya gana da Ministan Harkokin Wajen Kanada
2024-11-16 04:29:39 CMG Hausa
A jiya Juma'a 15 ga Nuwamba, bisa agogon Peru, ministan Harkokin Wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Kanada Stephen Jolly a Lima, hedkwatar kasar Peru.
Wang Yi ya bayyana cewa takunkumin karin haraji a kan motocin lantarki da kasar Sin ke kerawa ya karya kwarin gwiwar kuzarin gudanar da kasuwanci mai 'yanci. Don haka, ya kamata kasar Kanada ta bi ka'idoji da dokokin Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) tare da cire takunkumin da ta kakaba a kan kayayyakin kasar Sin.
A nashi bangaren, Stephen Joly ya ce Kanada tana tsayawa kan manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, kuma ta mayar da hankali sosai ga kyautata zumuncin dake tsakanin Kanada da Sin .
Ya kara da cewa, za a ci gaba da musayar ra'ayi tsakanin manyan kusoshin kasashen 2, da kuma shawo kan bambance-bambancensu yadda ya kamata. (Abdulrazaq Yahuza Jere)