logo

HAUSA

Cutar kyandar biri na ci gaba da bazuwa a sassan Afirka in ji jami’in cibiyar Africa CDC

2024-11-16 09:26:53 CMG Hausa

Babban daraktan cibiyar kandagarki da shawo kan yaduwar cututtuka ta Afirka ko Africa CDC mista Jean Kaseya, ya ce cutar kyandar biri na kara bazuwa a kasashen Afirka, watanni 3 bayan ayyana ta a matsayin cuta dake bukatar aiwatar da matakan gaggawa don shawo kan ta.

Mista Kaseya, ya ce a shekarar nan kadai, adadin wadanda suka harbu da cutar ya haura mutum 53,000, wanda hakan ke nuni ga kamarin bazuwarta.

Jami’in ya bayyana hakan ne yayin wani taron ’yan jarida da ya gudana ta kafar bidiyo da yammacin ranar Alhamis, inda ya ce a shekarar ta bana, kasashen Afirka 19 sun sanar da hasashen harbuwar mutane 53,903, ciki har da mutum 11,147 da aka tabbatar sun harbu da cutar, yayin da tuni ta hallaka mutane 1,109. Ya ce a makon jiya kadai, an samu hasashen harbuwa da cutar kyandar biki 2,836, ciki har da mutane 461 da aka tabbatar sun kamu da ita, da sabbin mutane 34 da cutar ta hallaka.

Africa CDC, ta ce alkaluman wadanda aka tabbatar sun harbu da cutar a sassan Afirka, sun karu a bana da kaso 569 bisa dari, kan jimillar na shekarar da ya gabata. Don haka mista Kaseya, ya bayyana bukatar fadada binciken lafiya, da bunkasa ayyukan samar da magungunan takaita tasirin cutar a cikin gida. (Saminu Alhassan)