logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbo wani sabon bashi na dala miliyan 134 domin bunkasa tsarin samar da irin shuka

2024-11-16 10:05:17 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karbo wani sabon bashi daga bankin raya kasashen Afrika da ya kai na dala miliyan 134 domin a taimakawa manoma wajen bunkasa sha`anin samar da irin shuka da kuma habaka noman abinci a kasa baki daya.

Ministan ma`aikatar gona da bunkasa samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 14 ga wata a Calabar ta jihar Cross Rivers yayin bikin kaddamar da shirin noman rani na shekara ta 2024 zuwa 2025.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan gonar ya ci gaba da cewa sakamakon bullo da shirin noman rani na kasa wanda ke da nufin yin noma babu kakkautawa a dukkan tsawon shekara, babu shakka bashin da aka ciwo zai kara bayar da kwarin gwiwa na kokarin da ake yi na wadata kasa da abinci.

Sanata Abubakar Kyari ya ce da ma dai tun a baya gwamnatin tarayya ta daura damarar gangamin noman abinci domin tabbatar da ganin kowanne dan Najeriya yana da ikon samun abinci mai gina jiki kuma cikin rahusa.

Ya kara da cewa gwamnati tana son ta yi amfani da bangaren noma wajen farfado da tattalin arzikin kasa, ta hanyar mayar da hankali sosai wajen kara adadin noman wasu nau`ikan kayan abinci, kamar Alkama da Shinkafa da Masara da Dawa da Waken suya da kuma Rogo a lokutan noman rani da na damuna.

Ministan gonar na tarayyar Najeriya ya ce a kwanan nan gwamnati ta agazawa manoma kusan dubu 193 a karkashin shirin noman damuna na shekara ta 2024 a jahohi 37 ciki har da Abuja. (Garba Abdullahi Bagwai)