Tashar Chancay: Sabon mafari ne ga “tsohuwar hanyar Inca a sabon zamani"
2024-11-16 01:31:42 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude tashar jiragen ruwa ta Chancay ta kasar Peru, ta kafar bidiyo, tare da takwararsa ta Peru, Dina Boluarte, a fadar shugabacin kasar Peru dake Lima, hedkwatar kasar, a ranar 14 ga wata, bisa agogon wurin.
Shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin bude tashar, kuma wannan shi ne babban sakamako da aka cimma yayin da shugaba Xi ya kai ziyarar aiki a Peru, sannan kuma yana nuna kyakkyawar alaka ta dogon lokaci tsakanin al'ummun kasashen biyu.
“Daga Chancay zuwa Shanghai”, ya riga ya zama wani karin magana dake samun karbuwa, wanda ya nuna fatan jama'a game da wannan sabuwar hanyar ta kan-tudu da ta teku, wadanda suka hada shiyyoyin Asiya da Latin Amurka da kasashen Caribbean a cikin sabon zamanin da muke ciki. Wannan kuma ya shaida ra'ayin bangarorin Sin da Peru game da sabon yanayi na karuwar tattalin arzikin kasa da kasa, da kuma niyyar bangaren Peru ta shiga babbar kasuwar Sin. Tashar Chancay ba kawai sabon mafari ne ga “tsohuwar hanyar Inca a sabon zamani" ba, har ta kasance wani sabon babi ne na rayuwar al'ummar Latin Amurka da Caribbean mai dadi.
A yayin ziyarar aiki ta shugaba Xi, shugabannin kasashen Sin da Peru sun rattaba hannu kan wasu muhimman takardu na hadin gwiwa, kamar shirin hadin gwiwar gina Ziri Daya da Hanya Daya, da takardar inganta yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci. Bangarorin biyu sun fitar da sanarwa ta hadin gwiwa a kan tsara shirye-shiryen zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare tsare.
Daga bude tashar Chancay zuwa inganta yarjejeniyar ciniki cikin 'yanci, da ci gaba da inganta tattaunawa da hadin gwiwa a fannonin ilimi, al'adu, yawon bude ido da dai sauransu, zuwa mutunta ra'ayin bangarori daban daban, da ba da shawarar yin hadin gwiwa tsakanin bangarori daban daban, dukkansu sakamako ne da ziyarar aiki ta shugaba Xi ta samu, wacce ta zurfafa alaka mai dogon tarihi da ke tsakanin Sin da Peru, kana ta kara fadada sararin yin hadin gwiwa ta cin moriyar juna, ta kuma ba da sabuwar ma'ana ga dangantakar bangarorin biyu a sabon zamani, sannan ta kara sa kaimi ga hadin gwiwa tsakanin Sin da Latin Amurka da Caribbean, da tabbatar da bunkasar kasashe masu tasowa na duniya.(Safiyah Ma)