Majalissar zartaswa ta Najeriya ta amince da shawarar tsayar da naira tiriliyan 47.9 a matsayin kasafin kudin 2025
2024-11-15 09:19:50 CMG Hausa
Majalissar zartaswa ta gwamnatin tarayyar Najeriya ta amince da shawarar gabatar da naira tiriliyon 47.9 a matsayin kudurin dokar kasafin kudin badi na 2025.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa Alhaji Atiku Bagudu ne ya tabbatar da hakan jiya Alhamis 14 ga wata a birnin Abuja, bayan kammala taron majalissar wanda aka gudanar karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
A lokacin da yake karin haske ga manema labarai dake fadar shugaban kasa, ministan ya ce, haka kuma taron majalissar ya amince da tsarin gudanar da matsakantan ayyuka tsakanin shekara ta 2025 da 2027.
Alhaji Atiku Bagudu ya ci gaba da bayanin cewa, gwamnati za ta yi la’akari da farashin gangar mai a kan dala 75 a kasafin kudin na badi, sannan kuma an yi hasashen za a rinka hako gangar mai miliyan 2 a kullum, sabanin miliyan 1.8 da ake hakowa yanzu haka.
Ha’ila yau kuma an tsayar da farashin dala a kan naira 1,400, sannan kuma gwamnati ta ci burin samun karin kaso 6.4 na kayayyakin da ake sarrafawa a cikin gida.
Taron majalissar zartaswar na jiya ya kuma yi duba a kan yadda aka aiwatar da kasafin kudin shekara nan da muke ciki ta 2024, sannan kuma a saka dan ba a kan yadda za a tinkari kasafin kudin badi wanda ake sa ran kammala shirye-shiryen gabatar da shi ga zauren majalissar dokokin kasar a karshen watan Disambar shekarar nan ta 2024. (Garba Abdullahi Bagwai)