logo

HAUSA

Kamfanonin wayoyin sadarwa na kasar Sin na fatan fadada kasuwanninsu a nahiyar Afirka

2024-11-15 09:28:47 CMG Hausa

Yayin bikin baje hajojin fasaha na “Africa Tech Festival” na bana, wanda ya gudana a babban zauren gudanar da taruka na kasa da kasa dake birnin Cape Town na Afirka ta kudu, an baje hajoji masu dauke da sabbin fasahohin kirkire-kirkire, kuma kamfanonin kasar Sin dake taka rawa a wannan fanni, sun bayyana fatansu na fadada kasuwanci a sassan nahiyar Afirka.

Bikin na baje fasahohi, wanda ya gudana tsakanin ranakun Talata zuwa jiya Alhamis, shi ne mafi girma da tasiri a fannin baje hajojin fasaha a Afirka, kuma a bana ya tara mahalarta 15,000, da masu baje hajoji sama da 300, da masu gabatar da jawabai 450 daga sassan Afirka, da ma kasashen wajen nahiyar.

Da yake tsokaci game da bikin, shugaban kamfanin kera wayar salula ta Honor reshen kasar Afirka ta kudu Fred Zhou, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, "Nahiyar Afirka kasuwa ce mai kyakkyawar makoma, kuma muna da matukar kwarin gwiwa game da kasuwar Afirka ta kudu da ma nahiyar Afirka baki daya". 

Fred Zhou ya kara da cewa, a matsayinsa na kamfanin kasar Sin, a duk shekara, Honor na samar da guraben ayyukan yi sama da 300 a Afirka ta kudu. Kazalika, kamfanin na fatan zama wata gada da za ta hade Sin da Afirka ta kudu. Ya ce burin kamfanin shi ne taimakawa masu amfani da wayoyin salula na Afirka ta kudu da damar gaggauta rungumar wannan zamani ya dijital. (Saminu Alhassan)