Adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa a Sin tsakanin Janairu da Oktoban bana ya kai biliyan 3.71
2024-11-14 20:28:10 CMG Hausa
Adadin zirga-zirgar fasinjoji ta jiragen kasa a kasar Sin, tsakanin watan Janairu da Oktoban bana ya kai matsayin koli, inda alkaluma suka nuna adadin ya kai biliyan 3.71, karuwar da ta kai ta kaso 13 bisa dari a shekara.
Kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na kasar Sin ne ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yana mai cewa zirga-zirga ta layukan dogo na kasar ta gudana lami lafiya bisa tsari cikin wannan wa’adi. (Saminu Alhassan)