logo

HAUSA

Kamfanin Joy Billiards na kasar Sin na yunkurin neman a sanya wasan Snooker nau’in “heyball” cikin gasannin kasa da kasa

2024-11-14 21:05:40 CMG Hausa

Kamfanin Joy Billiards na kasar Sin, wanda ke samar da teburan wasan kwallon Snooker, ya haskaka a yayin babban taron masu ruwa da tsaki na kasa da kasa a fannin wasan Snooker ko ANOC, wanda ya gudana a kasar Portugal, lokacin da kamfanin ya gabatar da nau’in wasan Snooker na “heyball” wanda a ake amfani da kwallayen Snooker 8 sabanin sauran nau’o’in wasan, ga shugabannin duniya masu ruwa da tsaki a harkar wasan, yana mai neman a shigar da nau’in Snooker na “heyball” cikin wasannin da za a rika yi yayin gasar Olympic.

Taron na ANOC karo na 27 da ya gudana a birnin Cascais na kasar Portugal, ya hallara masu ruwa da tsaki daga sassa daban daban, inda aka tattauna sosai game da harkokin da suka shafi gasar Olympic, da hadin gwiwar gudanar da wasannin kasa da kasa, da ma tsara yadda za a gudanar da gasannin dake tafe.

A matsayin kamfani mai hadin gwiwa da ANOC, wajen karbar bakuncin taron na bana, kamfanin Joy Billiards, wanda daya ne daga kamfanonin Sin dake jagorantar harkar kera teburan wasan Snooker a duniya, kamfanin ya yi amfani da damar taron na bana wajen nuna yadda wasan “heyball” yake ga sama da wakilan kwamitin shirya gasar Olympic ta kasa da kasa su sama da 200. Wanda hakan ya yi daidai da burin da ake son cimmawa na yayata wasan “heyball”, da ma kokarin sanya shi cikin jerin wasannin da ake yi a gasar Olympic.

Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin wato Xinhua, mamallakin kamfanin Joy Billiards Qiao Yuanxu mai shekaru 72 a duniya, ya ce "Mun zo wurin da ya dace, domin yayata “heyball” a matakin kasa da kasa, burin mu shi ne haduwa da jami’ai daga dukkanin sassan duniya, kuma babban taron nan na ANOC dama ce ta cimma wannan buri."

Wannan taro na ANOC ya hallara wakilai daga kwamitocin shirya gasar Olympic na kasashe da yankuna har 200, an kuma saurari jawabai daga manyan kusoshi, ciki har da shugaban hukumar shirya gasar Olympic ta kasa da kasa ko IOC mista Thomas Bach, wanda ke halartar taron ANOC na karshe kafin kammalar wa’adin aikinsa.

Yayin wani taron tattaunawa da ya gudana a gefen babban taron, kamfanin Joy Billiards ya shirya wani wasan nuna fasahohin gasar snooker, wadda manyan kwararru na kasa da kasa a wasan irin su Mark Williams, wanda shi ma a yanzu ke cikin masu buga gasar “heyball” suka halartar, da mai rike da kambin duniya na wasan “heyball” Gareth Potts, da ma sauran kwararru da suka taba lashe gasannin kasa da kasa a matakin Olympic a sassan wasanni daban daban, sun hallara tare da nuna sha’awar su ga wasan na “heyball”.

A cikin tsokacin sa mamallakin kamfanin Joy Billiards, mista Qiao Yuanxu ya ce "Abun burgewa ne ganin manyan ‘yan wasan Olympic suna gwada wasan “heyball”, damar da muka samar ta cudanya da juna, ta baiwa wakilai zarafin koyon wasan kai tsaye, tare da gwada fasahohinsa, wanda hakan ya haifar da tattaunawa game da wasan". Wannan dama ta nuna fasahohin “Heyball” a wurin babban taro, ta kara janyo ra’ayin bangarori daban daban, inda wasu daga wakilai da suka hallara suka rika tambaya game da dokoki da kuma banbancin sa da sauran wasanni dangin kwallon Snooker.

A nasa tsokaci game da alakar ANOC da kamfanin Joy Billiards, babban sakataren ANOC Gunilla Lindberg, ya ce yarjejeniyar hulda tare ta shekaru 4 da suke aiwatarwa, ta nuna kwazon ANOC don gane da kyautata hadin gwiwa da shugabannin masana’antu masu nasaba da wasan Snooker.

Tun da farko dai kamfanin Joy Billiards, ya fara taka rawa a fannin ne sakamakon yadda ya rika samar da teburan wasan Snooker masu matukar inganci, kafin daga bisani ya fara tallafawa wasanni ta hanyar daukar nauyin gasanni.

Game da hakan, Qiao ya ce "Mun sake zuba jarin ribar da muke samu wajen shirya manyan gasannin “heyball”, wadannan wasanni ba kawai sun daukaka sunan kamfanin mu ba ne, har ma sun yayata wasan “heyball” a matakin kasa da kasa."

Cikin shekarun baya bayan nan, wadannan gasanni sun fadada daga wadanda ake yi a matakin kasa zuwa na kasa da kasa, wanda hakan ya sa ake kallon gasar cin kofin "The Joy Cup", daidai da sunan gasar “heyball”. Kuma a bangaren mista Qiao, burinsa shi ne fadada darajar wannan gasa ta “heyball” zuwa matakin Olympic.

Qiao ya bayyana cewa, lokacin da gwarzon gasar Snooker na shekarar 2005 wato Ding Junhui, ya yi tsokaci a dandalin kasa da kasa na wasan, ya bayyana fatan ganin wata rana sabbin nau’o’in wasannin Snooker za su kai ga matsayin gasar Olympics, yana mai fatan “heyball” zai share fagen hakan.

An dai jima ana ta yunkurin sanya gasar wasannin Snooker cikin gasar Olympics. Har ma hukumar shirya gasannin Snooker ta duniya ko WCBS, wadda ta samu amincewa daga hukumar IOC a shekarar 1998, da fari ta mika bukatar hakan, ciki har da sanya daya daga gasannin cikin gasar Olympics ta Tokyo ta 2020, amma a lokacin hakan bai yiwu ba.

A wannan gaba da wasan “heyball” ke kara samun tagomashi, kamfanin Joy Billiards ya kara kaimin yayata wasan. Kuma cikin burin da kamfanin ke fatan cimmawa nan zuwa shekarar 2032, lokacin da za a gudanar da gasar Olympics ta birnin Brisbane na Queensland, akwai zuba jarin da yawan sa ya kai sama da dalar Amurka miliyan 6, a matsayin kudaden rabawa masu lashe gasannin kasa da kasa dake tafe, ta yadda hakan zai haifar da tushe mai karfi na shirya gasanni.

Yanzu haka dai wasan Snooker na "Heyball”, ya riga ya shiga cikin wasannin tebur na kasa da kasa, kuma za a gudanar da shi a yayin gasar wasannin duniya na badi a birnin Chengdu na kasar Sin.

Game da hakan, Qiao ya ce “Burin mu shi ne wasan ya karbu cikin gasannin da ake gudanarwa a yankunan kudu maso gabashin Asiya, da na Asiya."

A kasar Portugal, Qiao ya jaddada wannan buri, wanda ya yi matukar jan hankalin mahalarta, ciki har da shugaban IOC mista Bach, wanda ya yi matukar nuna sha’awar jawabin.

Qiao ya ce "Mun fara daga matakin farko har zuwa wannan matsaya, mun nunawa wakilai mahalarta wannan taro daga kasashe da yankuna sama da 200 wasan “heyball”, yanayin ya yi kama da mafarki a gare ni. Wannan tafiya ce ta wani kamfanin samar da kayayyakin wasa na kasar Sin, wadda ke kunshe da ruhin juriya da fatan cimma burin Olympic".