logo

HAUSA

Salon zamanantarwa irin na kasar Sin riba ce ga duniya baki daya

2024-11-14 16:06:59 CMG Hausa

A yayin zaman dandalin masana da kwararru na ’yan jaridu daga kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasar tattalin arziki da ya gudana a birnin Sao Paulo na kasar Brazil a farkon makon nan, an fitar da rahoton hadin gwiwa mai taken "Sabon salon ci gaban bil Adama da muhimmancin hakan ga bunkasar duniya". 

Rahoton wanda kwararru daga cibiyar nazarin tarihin JKS da binciken adabi, da hadin gwiwar kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua suka fitar, ya yi cikakken fashin baki game da ma’ana, da dabarun aiwatarwa, da muhimmancin dake kunshe cikin salon zamanantarwa irin na kasar Sin, tare da abun al’ajabi da kasar Sin ta cimma a fannin bunkasa rayuwar bil Adama.

Idan mun yi nazari da kyau, za mu ga cewa wannan sabon salon samar da ci gaba dake kunshe cikin tsarin zamanantarwa irin na kasar Sin, ya yi daidai da burin kasar na ganin an shawo kan manyan kalubalolin dake addabar dan Adam a wannan karni na 21.

A halin da duniya ke ci yanzu, sauye-sauye da suke faruwa sun tilasawa al’ummun duniya shiga wani yanayi mai sarkakiya, inda dukkanin sassa ke mayar da hankali ga tambaya kan abubuwan dake addabar duniya da abubuwan da ya dace a yi domin warware matsaloli, kasancewar hakan ne zai haifar da ci gaban da dan Adam ke fata, da kuma dorewar rayuwa mai inganci a yanzu da ma a nan gaba.

Bisa wannan buri, JKS ta jagoranci al’ummar Sinwa wajen samar da daidaiton ci gaba ta fuskar farfado da kai, da inganta tsarin siyasa, da raya al’adu, da zamantakewa, da kare muhalli da sauransu. Wannan sabuwar turba ta zamanantarwa irin ta Sin ta bayar da gudummawar kawar da gibin jagoranci, ta wanzar da aminci, da zaman lafiya da ci gaba, tare da samarwa duniya wata alkibla ta cimma zaman lafiya da makoma mai haske a fannin wayewar kan daukacin bil Adama.

A wannan gaba da kasar Sin mai al’ummun da yawansu ya haura biliyan 1.4 ke kan turbar zamanantar da kai, kasar na kan wata turba ta baiwa duniya kyakkyawan misalin zamanantarwa a sabon zamani. 

Ko shakka babu cimma nasarar zamanantar da kai, buri ne na dukkanin kasashen duniya, kuma muddin duniya ta rungumi misalin irin nasarori da kasar Sin ta cimma a wannan fage hannu biyu, al’ummar duniya musamman kasashe masu tasowa, da su kai ga cimma burinsu na samun ci gaba yadda ya kamata.