logo

HAUSA

Adadin lantarki da Sin ke samarwa ta makamashin nukiliya ya kai matsayin koli a duniya

2024-11-13 20:15:48 CMG Hausa

 

Adadin lantarki da kasar Sin ke samarwa ta makamashin nukiliya, ciki har da wanda ake aiki da shi, da wanda ake kan ginawa, da wanda aka amince da shi a hukumance, ya kai matsayin koli tsakanin kasashen duniya.

A cewar shugaban kungiyar nazarin makamashi ta kasar Sin ko CERS a takaice, mista Shi Yubo, kasar Sin na da kilowatts miliyan 58.08 na lantarki daga nukiliya da ake amfani da shi, da kilowatts miliyan 55.05 da ake kan ginawa a hukumance, wanda hakan ya sanya kasar zama na daya a duniya a wannan fanni.

Shi Yubo, ya bayyana hakan ne yayin taron karawa juna sani karo na 3, game da bunkasar ingancin makamashin nukiliyar kasar Sin, wanda ya gudana a birnin Shenzhen, na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin, tsakanin ranakun Litinin zuwa Larabar nan.

Shi ya kara da cewa, abu ne mai muhimmanci a mayar da hankali sosai ga ingiza sabon karsashi, a fannin samarwa da bunkasa ingancin sashen makamashin nukiliyar kasar Sin zuwa matsayin koli. (Saminu Alhassan)