Babban jami’in Sin ya halarci taron kolin shugabannin kasa da kasa kan daukar matakan daidaita sauyin yanayi
2024-11-13 20:46:29 CMG Hausa
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin firaministan kasar Ding Xuexiang, ya halarci taron kolin shugabannin kasa da kasa kan daukar matakan daidaita sauyin yanayi da ake yi a birnin Baku, hedkwatar Azerbaijan, inda ya gabatar da jawabi.
A cikin jawabin na sa, Ding ya bayyana cewa, domin karfafa tsarin kula da batun yanayi na duniya, ka'idar daukar nauyi tare ita ce ginshiki. Ya ce bangaren Sin yana kira ga kasashe masu sukuni, da su kara yawan tallafin kudi, da fasahohin zamani ga kasashe masu tasowa. Kazalika kasar Sin tana son yin aiki tare da dukkan bangarori, bisa jagorancin manufar gina al'umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil'adama, don kare gida daya na bil'adama tare, da kuma gina duniya mai tsafta da kyau. (Safiyah Ma)