logo

HAUSA

Xi ya taya jami’ar Sun Yat-sen murnar cika shekaru 100 da kafuwa

2024-11-12 15:06:36 CMG Hausa

 

Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aike da wasikar taya murna ga jami’ar Sun Yat-sen bisa cikarta shekaru 100 da kafuwa, a yau Talata.

Xi ya bukaci jami’ar ta shigar da ci gaban da ta samu cikin manyan tsare-tsaren ciyar da kasa gaba da kuma bukatun da ake da su a shirin samar da gawurtaccen yankin Guangdong-Hong Kong-Macao mai ci gaba.

Ya kara da cewa, ya kamata jami’ar ta kara himma da kwazon gina kanta zuwa matsayin jami’ar da ta amsa sunanta a duniya mai kunshe da tsare-tsaren Sinawa, da kuma bayar da gudunmawa mai muhimmanci ga zurfafa zamantarwar Sinawa.

Jami’ar Sun Yat-sen dai, gwarzon juyin-juya-halin demokuradiyyar kasar Sin Sun Yat-sen ne ya kafa ta kuma aka sa mata sunansa. Marigayi Sun ne ya jagoranci juyin-juya-halin shekarar 1911 da ta kawo karshen shekaru 2,000 na mulkin sarakunan gargajiya a kasar Sin.

Wacce aka kafa a 1924, jami’ar ta yaye fiye da kwararru 800,000 a sassa daban-daban na ilimi a tsawo tarihin kafuwarta na shekaru 100. (Abdulrazaq Yahuza Jere)