logo

HAUSA

Falasdinu: An yi taron tunawa da cika shekaru 20 da rasuwar Yasser Arafat

2024-11-12 14:06:54 CMG Hausa

 

A ranar 11 ga watan Nuwamba, Falasdinawa sun yi taron tunawa da kuma cika shekaru 20 da rasuwar tsohon shugaban Falasdinu, marigayi Yasser Arafat, a wasu sassan gabar yamma ta kogin Jordan.

A birnin Ramallah a gabar yamma ta kogin Jordan, daruruwan Falasdinawa sun yi gangami a dakin tunawa da marigayi Yasser Arafat, tare da daukar tutocin Falasdinu da hotunan Arafat.

A daren ranar 10 ga wata kuma, shugaba Mahmoud Abbas na Falasdinu ya yi jawabin tunawa da Arafat ta kafar talibijin, inda ya ce, Falasdinawa dake zirin Gaza suna fama da bala’in da ba a taba ganin irinsa ba, amma duk da haka ba za su bar kasarsu ta asali ba, kuma wannan buri ne na marigayi Yasser Arafat da dukkan Falasdinawan da aka kashe su.

A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2004, Yasser Arafat, wanda yake daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar Fatah, ya rasu a kasar Faransa, yana da shekaru 75. (Tasallah Yuan)