Dan kasuwan Najeriya: Dole a jinjina wa kasar Sin bisa yadda ta bude kofofi ga kasashen waje
2024-11-12 16:10:26 CMG Hausa
Usman Sa’id Sufi, dan kasuwan Najeriya ne da ya shigo birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, don halartar bikin baje-kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na 7, ko kuma CIIE a takaice.
A zantawarsa da Murtala Zhang, Usman Sa’id Sufi ya yi tsokaci kan muhimmancin bikin, da kuma abubuwan da ya kawo don baje-kolinsu a wannan karo, inda ya ce, manoman Najeriya za su ci gajiya sosai daga harkokin fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya, ciki har da kasar Sin.
Malam Usman, wanda ya taba zuwa kasar Sin a lokutan baya, ya kuma bayyana yadda ci gaban kasar Sin ya burge shi matuka. (Murtala Zhang)