logo

HAUSA

An Bude Rumfar Kasar Sin A Babban Taron Sauyin Yanayi Na COP29 A Baku

2024-11-12 12:42:09 CMG Hausa

A jiya Litinin ne aka bude rumfar kasar Sin a babban taron Majalisar Dinkin Duniya a kan Sauyin Yanayi da aka yi wa lakabi da “COP29” da ke gudana a Baku da ke kasar Azerbaijan.

Rumfar kasar Sin za ta karbi bakuncin tarurruka na kwana 10 da za su kunshi harkoki daban-daban a yayin babban taron na Kasashen Duniya da Suka Amince da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya a kan Sauyin Yanayi karo na 29 wanda zai gudana daga ranar 11 zuwa 22 ga Nuwamba.

Da yake jawabi a gefen taron da ya alamta bude rumfar, shugaban tawagar wakilan kasar Sin a babban taron na COP29 wanda har ila yau shi ne mataimakin ministan Ma’aikatar Kula da Al’amuran Halittun Doron Kasa da Muhalli, Zhao Yingmin ya ce, kasar Sin ta kasance babbar kusa a cikin mahalarta taron, mai ba da gudunmawa kuma jagora a bangaren wayewar kan duniya a kan abin da ya shafi halittun doron kasa a ’yan shekarun da suka gabata.

Shi kuwa babban jakadan kasar Sin a kan sauyin yanayi, Liu Zhenmin, cewa ya yi, a ko yaushe kasar Sin tana ba da fifiko a kan shawo kan matsalar sauyin yanayi inda take daukar hakan a matsayin muhimmin lamarin da ya shafi kasa. Ya kara da cewa, dukufar da kasar Sin ta yi ga habaka samar da tsaftar muhalli da rage fitar da hayaki mai guba ta haifar da da-mai-ido tare da samun yabawa daga kasashen duniya.

Bugu da kari, Liu ya bayyana yakinin cewa taron na COP29 zai kara wa kasashen duniya kwarin gwiwa, kana ya jaddada muhimmancin rike alkawari a kan abin da aka cimma matsaya a kai da ya raba wa kowa hakkin da ke wuyansa da kuma tilasta aiki da yarjeniyoyin da aka shar’anta.

Ya kuma yi kira ga kasashen da suka ci gaba a duniya su sauke nauyin da ke wuyansu ta hanyar samar da tallafin kudi ga kasashe masu tasowa domin kara musu karfin shawo kan kalubalen sauyin yanayi. (Abdulrazaq Yahuza Jere)