logo

HAUSA

Kawancen jam’iyyun ’yan adawa ya lashe zaben ’yan majalisar dokokin kasar Mauritius

2024-11-12 16:43:05 CMG Hausa

Da sanyin safiyar yau Talata, kwamitin zabe na kasar Mauritius ya sanar da sakamakon zaben ’yan majalisar dokokin kasar, inda kawancen jam’iyyun ’yan hamayya dake karkashin jagorancin tsohon firaministan kasar, Navinchandra Ramgoolam, wato Alliance of Change, ya lashe zaben ’yan majalisar dokokin kasar bisa rinjayen kuri’un da ya samu a ranar 10 ga wata. Kana, a matsayin jagoran ’yan jam’iyyu dake samun rinjayen kujeru a majalisar, Navinchandra Ramgoolam zai zama sabon firaministan kasar.

Navinchandra Ramgoolam, mai shekaru 77 a duniya, da ne na tsohon firaministan kasar Mauritius, marigayi Seewoosagur Ramgoolam. Navinchandra Ramgoolam ya taba zama firaministan kasar Mauritius tun daga shekara ta 1995 zuwa ta 2000, kana, daga shekara ta 2005 zuwa ta 2014. (Murtala Zhang)