Bikin sabuwar shekara na al'ummar kabilar Miao
2024-11-12 16:09:11 CMG Hausa
Yadda al’ummar kabilar Miao ke shagulgulan murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyarsu a gundumar Leishan ta lardin Guizhou da ke kudu maso yammacin kasar Sin. Bikin sabuwar shekarar ya kasance kasaitacce kuma mashahuri ga ‘yan kabilar Miao, inda su kan yi shagulgula domin murnar samun girbi mai albarka da kuma yi wa kakanninsu addu’a. A shekarar 2008, gwamnatin kasar Sin ta sanya bikin cikin jerin muhimman al’adun gargajiya na kasar.