Firaministan Isra’ila ya dauki alhakin mummunan harin da aka kai ta na’urar karbar sako a kan Hezbollah
2024-11-11 15:48:24 CMG Hausa
A jiya Lahadi, firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fito fili a hukumance ya dauki alhakin kai mummunan harin nan da aka kitsa a kan Hezbollah a watan Satumba, inda dubban kananan na’urorin karbar sako (pager) suka tarwatse a sassan Lebanon da Syria.
“Ina so na kai hari bisa amfani da na’urar karbar sakon,” in ji Netanyahu a yayin gudanar da taron majalisar zartarwa. Ya kara da cewa, “Sai suka ce min a taron majalisar, kar ka yi hakan, Amurka ba za ta lamunta ba. Ni dai na yi biris da su,” in ji shi.
Wannan ne karon farko da wani jami’in Isra’ila ya fito fili ya bayyana rawar da Isra’ila ta taka a harin wanda cikin kankanin lokaci ya kara rura-wutar yakin da ake yi tsakanin Isra’ila da Lebanon wanda ya-ki-ci-ya-ki-cinyewa tun daga watan Oktoban 2023. (Abdulrazaq Yahuza Jere)