logo

HAUSA

An aikewa wasu Amurkawa masu asali daga Afirka da sakwannin nuna wariya bayan babban zaben Amurka

2024-11-10 16:01:51 CMG Hausa

A cewar wasu rahotanni da dama daga kafofin watsa labarai, tun daga washegarin ranar babban zaben Amurka, wato daga ranar 6 ga watan nan, wasu Amurkawa masu asali daga Afirka, dake zaune a jihohi a kalla 20 na kasar, suka fara samun sakwannin wayar salula, dake dauke da abubuwa na nuna bambancin launin fata. 

Sakwannin sun rika nuni da cewe "An zabe ku don tsinkar auduga a gonaki mafiya kusanci, da fatan za ku shirya." Wadannan sakwannin wayar salula marasa dauke da sunayen masu aikewa da su, sun haifar da hayaniya a Amurka, inda wasu Amurkawa masu asali daga Afirka suka yi tir da su, suna cewa ko kadan matsalar nuna bambancin launin fata ba ta sauya ba.

Tun daga karni na 18, sakamakon habakar ayyukan gona a kudancin Amurka, an yi safarar bakaken fata da dama don yin aiki tukuru, wajen tsintar auduga. Saboda haka, "bakaken fata masu tsinkar auduga", ta zama jumla da ake amfani da ita, a matsayin ra'ayin nuna bambancin launin fata a Amurka. 

Hukumar FBI, da sauran hukumomin da abun ya shafa, na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma har yanzu ba a tantance wadanda ke aikewa da sakwannin wayar salular ba.  (Safiyah Ma)