Xi ya sanya hannu kan kundin doka mai nasaba da yayata ka’idojin kyautata amfani da makaman soji
2024-11-10 16:12:13 CMG Hausa
Shugaban kasa kuma shugaban hukumar zartaswa ta rundunar sojojin kasar Sin Xi Jinping, ya sanya hannu kan kundin doka mai nasaba da yayata ka’idojin kyautata amfani da makaman soji.
Wata sanarwar hukuma da aka fitar a jiya Asabar, ta ce dokar za ta fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Disamba mai zuwa. Kundin dokar mai kunshe da ka’idoji 92, cikin babuka 8, ya mayar da hankali ne ga fayyace matakan kasancewa cikin shiri, don cimma nasarar duk wani matakin soji, da ayyukan da suka rataya a wuyar rundunonin sojin kasar Sin a sabon zamani.
Kaza lika, a cewar sanarwar, ka’idojin za su samar da zarafi na kyautata tsari, da matakan samar da kayan aiki, da salon gudanarwa, da gyaran kayayyakin aikin soji, wadanda ake fatan za su ingiza cin gajiyar aiki da makamai, ko na’urorin soji bisa managarcin tsarin kirkire-kirkire. (Saminu Alhassan)