Ana tsare da wasu kwararru uku 'yan kasashe waje na kamfanin Resolute na kasar Australiya a Mali
2024-11-10 14:47:40 CMG Hausa
A kasar Mali, wasu 'yan kasashen waje guda uku ne dake aiki a kamfanin Resolute na kasar Australiya, dake mallakar wata mahakar zinari a kasar Mali, ake tsare da su a birnin Bakamo, a cewar hukumomin kasar a ranar jiya Asabar 9 ga watan Nuwamban shekarar 2024.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wannan dai shi ne karo na biyu a cikin wata guda da ake tuhumar ma'aikatan wannan kamfanin Resolute dake hakar ma'adinai.
Hukumomin kasar Mali na sanya ido tun zuwansu a kan karagar mulki a shekarar 2020, musamman ma a wannan bangare na arzikin karkashin kasa a Mali.
Inda tun a ranar 8 ga watan Nuwamban shekarar 2024, wasu kwararru uku 'yan kasar Australiya suka amsa kiran jami'an tsaro na PJ tun a yayin da suke a wani gidan otel dake birnin Bamako, tare da tura keyarsu a ofishin dake yaki da cin hanci da yi wa tattalin arziki zagon kasa, a cewar wata majiyar kotu.
Kamfanin Resolute na da hannun jari da kashi 80 cikin 100 a kamfanin dake kula da mahakar SYAMA dake kudu maso yammacin kasar Mali, yayin da gwamnatin Mali take rike da kashi 20 cikin 100.
Haka kuma, kamfanin Resolute na kasar Australiya na rike da wurin hakar zinari na Mako, a kasar Senegal makwabciya da kuma a kasar Guinee.
Hukumomin kasar Mali sun mai da yaki da cin hanci da neman 'yancin kasar kan albarkatun karkashin kasarta a matsayin wani ginshikin aikinsu na farko.
Sai dai, kamfanin Resolute na kasar Australiya ya bukaci da a gaggauta sakin ma'aikatansa, ganin cewa babu wani dalilin tsare su.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.