logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Borno za ta kara kulla alaka da bankin duniya da zummar farfado da harkokin tattalin arziki

2024-11-10 14:44:59 CMG Hausa

Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci samun kyakkyawar alaka da bankin duniya domin farfado da tattalin arzikin jihar, da ya samu koma baya sakamakon tashe-tashen hankula.

Gwamnan ya tabbatar da hakan ne ranar juma`a 8 ga wata a birnin Abuja yayin ganawar da ya yi da sabon darkatan bankin duniya a Najeriya Mr. Ndiame Diop, ya ce samun hadin kan bankin zai taimakawa tattalin arzikin jihar wajen murmurewa sosai.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Cikin wata sanarwa da babban mashawarcin gwamnan a kan harkokin yada labarai Dauda Iliya ya fitar, ta ambato gwamnan yana yabawa sosai bisa irin taimakon da yanzu haka banki na duniya ke baiwa jihar a bangarorin ilimi, aikin gona, kiwon lafiya da kuma bunkasa sha`anin kiwon dabbobi.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin jihar da bankin duniya a wadannan bangarori 4 babu shakka za su kawo cigaban jihar cikin hanzari.

Da yake nasa jawabin, sabon darkatan bankin na duniya a Najeriya Mr. Diop ya yaba mutuka bisa yadda gwamnatin jihar Bornon take yin cikakken amfani da tallafin da bankin ya kawo jihar domin sake gina bangarorin da suka lalace sakamakon hare-haren yan ta`adda, tare kuma da tallafawa rayuwar mutanen da tashe-tashen hankula ya shafa a jihar, inda ya ce hakika bisa yadda bincike ya nuna, jihar Borno ita ce jihar da take kan gaba wajen lura sawu da kafa ayyukan da bankin ke gudanarwa a tsakanin jahohin dake tarayyar Najeriya.

Haka kuma ya ce bankin zai taimakawa kokarin da jihar take yi wajen maganin cutar zazzabin cizon sauro da karfafa kiwon dabbobi, kasancewar jihar ta Borno ita ce ke samar da kaso 50 na dabbobi a shiyyar arewa maso gabas.

Daraktan bankin duniyar a Najeriya har ila yau ya ce ganin yadda yanzu aka samu zaman lafiya a jihar Borno, bankin zai kara fadada bayar da tallafin sa ga sauran bangarorin cigaba wadanda suke da tasiri na kai tsaye ga ci gaban yanayin rayuwar al`ummar jihar. (Garba Abdullahi Bagwai)