logo

HAUSA

Masana na ganin akwai kyakkyawar dama a dangantakar Sin da Najeriya

2024-11-09 16:39:16 CMG Hausa

Masana a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a jami’ar Abuja ta kasar Najeriya a ranar Alhamis, na sa ran daukaka matsayin dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Najeriya da aka yi a baya-bayan nan, za ta haifar da kyawawan sakamako, inda suka jaddada yiwuwar kara zurfafa hadin gwiwa.

A watan Satumban bana ne kasashen Sin da Najeriya suka daukaka huldar da ke tsakanin kasashen biyu zuwa cikakkiyar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, yayin ziyarar aiki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai Sin, a gefen taron kolin Beijing na dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika.

A wajen taron karawa juna sanin, masana sun bayyana fatansu na cewa, sabon matakin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zai sa kaimi ga ci gaban al'ummominsu.

Sheriff Ghali Ibrahim, wanda ya kafa cibiyar binciken harkokin yau da kullum ta Sin da Afirka a Najeriya, kuma mai karbar bakuncin taron ya ce, "Idan aka ce cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, ya kunshi abubuwa da dama, kamar gina amincewa da juna, baya ga haka, akwai kuma batutuwan hadin gwiwa da hadin gwiwar samun ci gaba." (Yahaya)