logo

HAUSA

Matasan Sinawa na rungumar tseren dogon zango

2024-11-08 15:00:42 CRI

Can a kan titin dake tsakanin filin wasanni na "Bird's Nest" dake birnin Beijing zuwa filin wasa na "Water Cube" dake filin Beijing Olympic Park, matashi Gong Zizhuo, dake karatun sarrafa sinadarai a jami’ar Peking, ya yi kokari matuka wajen kaiwa ga layin kammala tsere, yayin da ‘yan kallo ke masa shewa don karfafa masa gwiwa, a gasar tseren dogon zango ta Beijing Marathon.

Da yake tsokaci game da yadda tseren ya kasance gare shi, matashin ya ce "Ina ta duba agogo a lokacin da nake daf da kammala tseren. Buri na shi ne gamawa cikin sa’o’i 3, kuma na cimma nasarar hakan a birnin Beijing". Bayan kammala tseren, mashirya gasar sun aikewa Gong sakon waya dake nuna ya kammala cikin sa’o’i 2 da mintuna 56 da dakika 43.

Bisa rahoton ingancin ci gaba, da bincike kan wasannin gudu na kasar Sin na shekarar 2023, masu gudu dake tsakanin shekaru 40 zuwa 55, su ne suka fi yawa, inda matasa ke kara shiga wasanni da ake shiryawa a fannin, musamman a ‘yan shekarun baya bayan nan.

Tun fara karatun sa a kwaleji shekaru 3 da suka gabata, Gong ya lura da muhimmancin gudu a makaranta. Da fari, yana motsa jiki ne ta hanyar gudu da kewaya filin wasa, amma daga bisani sai ya rika bin sauran dalibai wajen kewaya fili sau 53, wanda hakan ke daidai da gudun rabin tseren “marathon”, kuma hakan ya bude babin shiga gasar tsere a gare shi.

Gong, wanda ya shiga gasannin tseren rabin dogon zango har sau 3 wato “half-marathon”, ya ce "Gudu yana sanya ni samun natsuwa, kana yana taimaka min wajen rage matsin rayuwa, ta yadda a lokacin da nake yin sa, nake iya ajiye duk wata damuwa, na samu natsuwa a zuciya ta. A wannan gaba da karin mutane ke komawa ga tsarin kula da lafiyarsu, adadi mai yawa na al’umma musamman matasa, na fita waje domin gwada tseren dogon zango."

Shi ma wani dalibin tarihi dake karatun digiri na 3 a jami’ar Tsinghua mai suna Cao Jiaxin, ya taka rawar gani a gasar da ta gudana cikin sa’o’i 3. Da yake bayyana yanayin gasar, matashi Cao mai shekaru 25 a duniya ya ce "Tun a jami’a na samu horo na, kuma na nuna kwazo na a gasar Beijing Marathon, wadda ita ma wata nasara ce gare ni, baya ga bincike da nake yi na karatu a yau da kullum".

Kamar dai shi kan sa binciken ilimi da nake yi, gudun tseren marathon shi ma aiki ne da ake shiryawa a tsaron lokaci. Akwai tsare tsare da akan yi tun da farko, kana akwai wasu kalubale yayin gudanar da shi.

Ya ce "Ina cikin harkar neman ilimi, malamai na, da abokai na suna karfafa min gwiwa idan na gaza. A gasar marathon ma, ‘yan kallo, da masu aikin sa kai, su ma sun rika yi min shewa da karfafa min gwiwa. A gaskiya, duk da hakan, ina dogaro ne da kwazon kai na wajen cimma nasarar shawo kan wahalhalun binciken ilimi, da tseren da na shiga na tsawon kilomita 42.195, inda na kammala sannu sannu bayan samun kwarewar tsere."

A matsayin sa na mai sha’awar wasan kwallon kafa, da wasannin motsa jiki, Cao ya fara tsere a matsakaicin mataki, da dogon zango akai akai tun daga shekarar 2022, kana ya shiga gasar tseren dogon zango a biranen Sin da suka hada da Nanjing, da Guangzhou da Wuxi. Yana yawan halartar kewayen wurin yin tsere, ko dakunan motsa jiki na cikin makaranta.

Domin shiryawa gasar tsere ta birnin Beijing, Cao ya rika yin atisaye na kwanaki 3 zuwa 4 a duk mako, da kuma gudun kilomita 30 domin sabawa da gudun dogon zango. Game da hakan ya ce "Na yi digirin farko cikin tsawon shekaru 4 a jami’ar Lanzhou, wurin dake da tudun sama da mita 1,500 a arewa maso yammacin kasar Sin. Idan da na mayar da hankali ga samun horo sosai, da yanzu ina iya yin gudu da sauri sosai,"

Ga ‘yan wasa masu sha’awar tseren dogon zango na kasashe duniya daban daban, titin birnin Beijing da ya tashi daga dandalin Tiananmen zuwa filin wasa na Beijing Olympic Park, ya kasance wuri mafi soyuwa gare su. Duk da cewa ‘yan tsere 30,000 ne suka halarci gudun, adadin wadanda suka yi rajista ya kai mutum 182,949 daga kasashe da yankuna 43, cikin kwanaki 3 da bude damar rajistar masu sha’awar shiga gasar a watan da ya gabata, ciki kuwa har da tarin matasa masu karatu a kwalejoji daga wasu biranen kasar Sin.

Geng Tao, wanda ya kammala karatu daga jami’ar Chongqing ya kammala tseren cikin sa’o’i 2 da mintuna 30 da dakika 27. Ya ce "Na so kammalawa cikin sa’o’i 2 da mintuna 30, amma na gaza da ‘yan dakikoki. Zan koma ci gaba da atisaye tare da abokanai na, don kara samun gogewa."

Game da wannan batu na tseren dogon zango, darakta a kungiyar tseren Marathon na birnin Beijing Zhao Fuming, ya ce a halin yanzu, karin makarantu suna shirya wasanni akai akai, suna karfafa gwiwar dalibai da su rika kula da koshin lafiyarsu ta gangar jiki da tunani. Samun nasarar daliban kwalejoji a fannin wasan tsere, na haifar da karin kwazon su a wasan, da ma wuraren ayyukan su a tsawon rayuwa."