Sin ta samu fadadar adadin sana’o’i da ake yiwa rajista
2024-11-08 15:16:24 CMG Hausa
Hukumar lura da ka’idojin kasuwa ta kasar Sin, ta ce adadin sana’o’in da aka yiwa rajista a kasar sun karu matuka, inda ya zuwa karshen watan Satumban bana suka kai miliyan 188, adadin da ya karu da kaso 3.9 bisa dari a shekara.
Cikin wannan jimilla miliyan 60.2 kamfanoni ne, yayin da sama da miliyan 125 kuma sana’o’i ne da mutane suka karkira da kan su, karuwar da ya kai ta kaso 6.1, da 3 bisa dari a shekara.
Ana danganta wannan ci gaba da aka samu da gaggauta samar da manufofi na fadada bukatun cikin gida, da ingiza karfin gwiwar jama’a, da karsashin sassan kasuwanni daban daban, wadanda suka haifar da bunkasar sassan sana’o’in kasuwanci daban daban a kasar ta Sin cikin rubu’i 3 na farkon shekarar nan. (Saminu Alhassan)