logo

HAUSA

Putin: hadin gwiwar Rasha da Sin yana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya

2024-11-08 20:07:10 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a birnin Sochi dake kudancin kasar Rasha a jiya ranar 7 ga wannan wata cewa, Rasha da Sin suna bukatar juna, kana hadin gwiwarsu yana da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya a duniya.

Shugaba Putin ya halarci taron shekara-shekara na kungiyar muhawara ta kasa da kasa ta Valdai ta kasar Rasha a wannan rana, yayin da ya amsa tambayoyi daga mahalartar taron, ya kuma bayyana cewa, Rasha da Sin suna da cikakken imani da juna a tarihi. Ya mai nuna yabo ga raya dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin bisa tushen yin imani da juna, kana ya yabawa tsarin tattalin arzikin kasar Sin, ya ce, Sin ta samu manyan nasarori kan samun bunkasuwa.

Putin ya kara da cewa, hadin gwiwar Rasha da Sin ya samar da yanayi wajen tabbatar da samun bunkasuwar kasashen biyu da tsaron lafiyar jama’arsu, kuma ba ya adawa da sauran kasashe. Ya ci gaba da cewa, Rasha da Sin sun yi atisayen soja na hadin gwiwa don tabbatar da tsaron kasashen biyu, ba kawo barazana ga saura ba, wannan mataki mai dacewa ne wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin har ma a duk duniya baki daya. (Zainab Zhang)