An fara zagaye na 2 na rigakafin cutar polio a Uganda
2024-11-08 10:35:54 CMG Hausa
Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Uganda ta kaddamar da zagaye na 2 na rigakafin cutar polio, wadda ake sa ran yi wa yaran kasar su miliyan 2.7 ‘yan kasa da shekaru 5.
Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce za a bi gida gida domin baiwa yara digo 2 na rigakafin kyauta a tsawon kwanaki 4, a aikin da zai karade gundumomin kasar 49.
A cikin watan da ya gabata ne aka gudanar da zagaye na farko na rigakafin, bayan bullar nau’i na 2 na Polio ko (cVDPV2), a watan Mayun da ya shude.
Rahotanni na cewa an gano sabon nau’in cutar ne a wata cibiyar tattara dagwalon ruwan bayi, dake Doko na gundumar Mbale a gabashin kasar ta Uganda. Kuma nan take aka fara shirin gudanar da alluran rigakafin cutar da nufin dakatar da bazuwar ta, a wani bangare na yaki da cutar polio na kasa da kasa karkashin hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da tallafin asusun kananan yara na majalissar.
A watan Oktoban shekarar 2006 ne WHO ta tabbatar da cewa Uganda ta kubuta daga cutar polio, bayan da aka shafe shekaru 10 ba a samu wani dan kasar dauke da cutar ba. (Saminu Alhassan)