logo

HAUSA

Makarantar nazarin al’adun gargajiya da wayewar kai ta kasar Sin dake Athens za ta habaka musayar al’adu

2024-11-08 13:37:56 CMG Hausa

A ranar Alhamis ce aka kafa makarantar nazarin al’adun gargajiya da wayewar kan Sinawa a yankin Athens, wacce ta zama tsangayar nazarin al’adun gargajiya da wayewar kai irinta ta farko da wata kasa daga yankin Asiya za ta kafa a kasar Girka.

Ana sa ran makarantar za ta karfafa bincike na ilimi da musanyar tarihi da wayewar kai a sassan duniya ta hanyar zakulo kayayyakin tarihi na zamanin baya, da shirya harkokin karatu, da kaddamar da horaswa da sauransu, kamar yadda wata sanarwa ta hukuma ta ayyana.

An sanar da kafa makarantar ce a yayin bude Babban Taron Duniya A Kan Nazarin Al’adun Gargajiya Da Wayewar Kai wanda ake gudanarwa a birnin Beijing daga ranar Laraba zuwa Juma’a. (Fassara: Abdulrazaq Yahuza)