logo

HAUSA

Babban hafsan hafsoshin sojin Isra’ila ya nemi a shirya fadada farmaki a Lebanon

2024-11-07 11:04:24 CMG Hausa

A jiya Larabar nan ne babban hafsan hafsoshin sojin Isra’ila Herzi Halevi ya bayyana cewa, wajibi ne sojojin kasar su kara shan damarar ci gaba da kai hare-hare a Lebanon, ciki har da fadada farmakin da suke kaiwa ta kasa.

“A yayin da ake kokarin cimma yarjejeniya ta hanyar difilomasiyya a Lebanon, wajibi ne mu kara shan damara a yakin da ake yi, musamman wajen fadada da rubanya farmakin da muke kaiwa ta kasa,” kamar yadda Halevi ya bayyana bayan tantance halin da ake ciki.

A wata sanarwa da aka fitar a hukumance, ya kara da cewa, “Za mu aiwatar da abubuwan da muka tsara ne a lokacin da muke da bukatar hakan”.

Halevi ya kuma nunar da cewa, a yayin da ake tsaka da kai hare-haren, Isra’ila ta kai farmaki a wuraren Hezbollah dake sassan kudancin Lebanon, kwarin Bekaa, Beirut da kuma Syria bisa yadda ta tsara. (Abdulrazaq Yahuza)