logo

HAUSA

Donald Trump ya lashe zaben shugaban kasar Amurka

2024-11-07 10:29:03 CMG Hausa

 

Bisa kididdiga da labarai da kafofin yada labarai da dama na Amurka suka bayar, an ce, yawan kuri’un da dan takarar jam’iyyar Republican ta Amurka, kana tsohon shugaban kasar Donald Trump ya samu ya riga ya wuce 270, wato adadin ya zarce yawan kuri’u da ake bukata. Ban da wannan kuma, jam’iyyar Republican za ta mallaki kujeru a kalla 52 a majalisar dattawa, adadin ya zarce rabi, za ta kuma samu ikon mulki.

A sanyin safiyar jiya Laraba, Trump ya gabatar da jawabi a cibiyar taro ta gundumar Palm Beach dake Florida, don sanar da nasararsa. A wannan rana kuma, shugaban kasa mai ci Joe Biden da mataimakiyar shugaban Amurka mai ci, kana ’yar takarar jam’iyyar Demokarat Kamala Devi Harris ta aike masa sakon taya shi murnar lashe zaben. Biden kuma ya gayyaci Trump zuwa fadar White House don tattauna aikin mika mulki.

Donald Trump mai shekaru 78 da haihuwa, zai kasance shugaba mafi tsufa idan ya kama aiki a watan Janairu mai zuwa.

Kafar watsa labarai ta CNN ta gabatar da sakamakon jin ra’ayin jama’a a ranar Talata da ta gabata, cewa kaso 40% na Amurkawa ba sa jin dadin halin da ake ciki yanzu a kasar, yayin da kashi 30% suka bayyana fushi game da hakan. Manazarta na ganin cewa, Amurkawa na fuskantar sabani, da fito-na-fito, da kiyayya tsakaninsu kan dimbin batutuwa, don haka akwai kalubaloli masu matukar tsanani ga sabuwar gwamnatin kasar. (Amina Xu)