Xi Jinping ya gana da firaministan Malaysia
2024-11-07 21:01:34 CMG Hausa
Da yammacin yau 7 ga wannan wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Malaysia Anwar bin Ibrahim dake ziyara a kasar Sin a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing. A yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasashen biyu su yi amfani da damar cika shekaru 50 da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakaninsu da kuma shekarar sada zumunta a tsakanin Sin da Malaysia wajen sa kaimi ga raya makomar bai daya ta Sin da Malaysia. (Zainab Zhang)