logo

HAUSA

Maraba Da Zuwan Bikin CIIE

2024-11-06 08:09:19 CGTN Hausa

A watan Mayun shekarar 2017 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a gun taron dandalin hadin gwiwar kasa da kasa na shawarar “ziri daya da hanya daya” cewa, kasar Sin za ta fara gudanar da baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE daga shekarar 2018. Shekaru shida a jere an gudanar da baje kolin CIIE cikin nasara, wanda ya kasance wani muhimmin mataki na dunkulewar tattalin arzikin duniya tare da bude kasuwannin kasar Sin ga duniya. 

Wannan ita ce shekara ta bakwai da kasar ke gudanar da baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na bakwai wanda aka fara daga ranar 5 kuma za a kammala a rana ta 10 ga wannan wata ta Nuwamba a birnin Shanghai. To, baje kolin na wannan karo ya yi maraba da shugabannin kasashen waje da dama wadanda suka hallara a bikin bude baje kolin da ma dubban masu baje kolin hajoji daga kasashen waje, wanda ke nuni da bunkasar dangantakar cinikayya, kuma ta tabbatar da kasar Sin a matsayin kasuwa mai girma. 

Kasashen Norway, Slovakia, Benin, Burundi da Madagaskar, da kuma asusun bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, za su hallara a baje kolin na CIIE a karo na farko, wannan ya kara tabbatar da muhimmancin da kasuwar kasar Sin ke da shi ga tattalin arzikin duniya. Kazalika, ta hanyar turjewa takunkumi da sauran manufofin kasashen yammacin duniya da ke inganta kariyar cinikayya, baje kolin CIIE ya kasance kofar da duniya ke bi wajen shiga kasar Sin, saboda masu baje kolin sun san cewa, ci gaban tattalin arzikin duniya ya ta'allaka ne ga yin cinikayya cikin 'yanci tare da kasar Sin. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Mohammed Yahaya)