Sin za ta yi amfani da cibiyar Mangrove ta duniya a matsayin wani dandali don sa kaimi ga ayyukan hadin gwiwa na duniya kan kare mangrove
2024-11-06 20:28:30 CMG Hausa
A yau Laraba ne aka gudanar da bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar kafa cibiyar Mangrove ta kasa da kasa a birnin Shenzhen da ke kudancin kasar Sin. Wakilai daga kasashe mambobi 18, wato rukunin farko na kasashe mambobin kungiyar, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar a hukumance, tare da kaddamar da allon cibiyar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a wannan rana cewa, kasar Sin za ta yi cikakken amfani da dandalin da cibiyar ta Mangrove ta kasa da kasa ta samar, wajen zurfafa mu’amala da hadin gwiwa da dukkan bangarori, da ciyar da hadin gwiwar duniya gaba wajen kare Mangrove, da kara inganci da karkon muhallin gandun dajin Mangrove don amfanin mutane a duk fadin duniya.
Shugaba Xi Jinping ne ya gabatar da shawarar kafa cibiyar Mangrove ta kasa da kasa a gun taro karo na 14 na kasashe masu sa hannu kan yarjejeniyar kiyaye fadamu a watan Nuwamban shekarar 2022, kuma ya samu karbuwa sosai tare da goyon bayan kasashen duniya. (Yahaya)