logo

HAUSA

Xi Jinping ya bayyana wajibcin nacewa ga tsarin mulki na gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin

2024-11-06 15:44:53 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni kan hidimtawa al’umma, inda ya ce hidimtawa al’umma muhimmin bangare ne na harkokin kasar Sin, kuma yana da alaka sosai da mulkin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da samun jituwa mai dorewa. Haka kuma yana da muhimmanci sosai ga zaman lafiya da ingantuwar rayuwar jama’a.

Xi ya jadadda cewa, hidimtawa al’umma nauyi ne dake wuyan JKS, kuma dole ne hukumomi daban-daban na jam’iyyar su sauke nauyin dake wuyansu don gaggauta ba da jagoranci da tabbatar da manufofin da kwamitin tsakiyar JKS ya yanke game da wadannan ayyuka. Ban da wannan kuma, ya ce kamata ya yi wurare daban-daban da hukumomi masu ruwa da tsaki su hada gwiwa, ta yadda za a mai da hankali ga sa ido kan wasu sana’o’i tare da raya harkokin jam’iyyar, yana cewa ta hakan za a iya kara azama wajen hidimtawa al’umma tare. Dadin dadawa, hukumomin su shirya taka rawar gaggauta raya kasa mai karfi da farfado da al’umma a dukkan fannoni bisa tsarin zamanintar da al’umma.

An yi taron hidimtawa al’umma na kwamitin tsakiyar JKS daga ranar 5 zuwa 6 ga wannan watan da muke ciki, inda aka sanar da muhimmin umurnin Xi Jinping. (Amina Xu)